1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu a Najeriya ta yanke wa 'dan kasar Sin hukuncin kisa

March 26, 2024

Kotun jihar Kano ta yanke wa wani 'dan kasar Chaina Frank Geng-Quangrong, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe budurwarsa a jihar Kano.

Wasu lauyoyin Kano a yayin zaman kotu.
Wasu lauyoyin Kano a yayin zaman kotu.Hoto: REUTERS

Kotun ta samu Frank Geng-Quangrong, da laifin kashe budurwarsa mai suna Ummukulsum Sani da ka fi sani da Ummita a watan Satumbar shekara ta 2022 a jihar Kano.

Karin bayani: Kotu ta yanke hukuncin kisa kan makashin Hanifa

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa za a gaggauta yanke masa hukunci idan har ya gaza daukaka kara kan hukuncin da kotun da ke zamanta a jihar Kano ta yi.

Karin bayani: Kano: Hukuncin kisa ga Sheikh Abduljabbar

Babu wanda ya fi karfin doka kuma dole ne kowa ya yi amfani da dokoki da al'adu na al'ummar jihar Kano ba tare da la'akari daga inda ya fito ba, acewar kwamishin shari'a na jihar Kano Barista Haruna Isa Dederi.