1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Dage shari'ar 'yan farar hulla da ke tsare

Salissou Boukari
July 3, 2018

A wannan talatan ce wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta dage shari'ar da ta kamata ta yi wa shugabannin kungiyoyin fararan hulla da ake tsare da su tun daga watan Maris da ya gabata.

Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

Kotun dai ta dage shari'ar har ya zuwa ran 10 ga wannan wata na Yuli, sai dai ba tare da ta sanar da dalilai ba. Rahotanni sun ce 'yan kungiyoyin fararan hullan da ta kamata a yi wa shari'ar ba a ma zo da su a kotun ta Yamai ba, amma dai magoya bayansu sun yi cika harabar kotun domin nuna goyon baya ga jagororin nasu.

Akalla mambobin kungiyoyin fararan hulla guda 26 suke tsare a gidajen kaso daban-daban wadanda akasarin su an kama su tun a ranar 25 ga watan Maris bayan wata zanga-zanga da ta haifar da dauki ba dadi tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, inda suke nuna adawarsu ga dokar kasafin kudin kasar ta wannan shekara ta 2018 da suka ce ta sabawa halin rayuwar 'yan kasar ta Nijar.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a wannan rana ta Talata, kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International, ta yi kira da a saki wadannan 'yan fararan hulla ba tare da gindaya wani sharadi ba.