1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu a Senegal ta mayar da Ousmane Sonko cikin 'yan takara

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 14, 2023

Magoya bayan Sonko da dama ne suka yi dafifi a harabar kotun Alhamis din nan a Dakar babban birnin kasar, mafi akasarinsu matasa suna ta murnar jin sakamakon hukuncin

Hoto: SEYLLOU/AFP/Getty Images

Kotu a Senegal ta umarci a mayar da sunan jagoran adawar kasar Ousmane Sonko mai shekaru 49 da haihuwa cikin jerin 'yan takarar shugabancin kasar a zaben badi, duk kuwa da cewa har yanzu yana kurkuku a daure.

Karin bayani:Kotun ECOWAS za ta yanke hukunci kan makomar takarar Sonko

Magoya bayan Sonko da dama ne suka yi dafifi a harabar kotun Alhamis din nan a Dakar babban birnin kasar, mafi akasarinsu matasa suna ta murnar jin sakamakon hukuncina cewa har yanzu yana kurkuku a daure.

Karin bayani:Senegal: Kalubalen mata manoma a karkara

A cikin watan Yunin da ya gabata ne dai wata kotun ta zartar wa Ousmane Sonko hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari, sakamakon zarginsa da laifin tunzura matasan kasar.