1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Kotun Sri Lanka ta samu mutane 14 da laifin kashe mutane 279

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 22, 2026

Kotun ta ce nan gaba za ta sanar da lokacin yanke hukunci a kan laifin da mutanen suka aikata.

Yadda wani 'dan sanda a Sri Lanka ke gadin wata mujami'a.
Yadda wani 'dan sanda a Sri Lanka ke gadin wata mujami'a.Hoto: Eranga Jayawardena/AP/picture alliance

Kotu a Sri Lanka ta samu mutane 14 da hannu dumu-dumu, kan lafin kashe mutane 279 a kasar, sakamakon harin ta'addancin da suka kai a ranar bikin Easter na shekarar 2019.

Karin bayani:Rikicin gidan yari ya yi ajalin fursunoni 19 a Sri Lanka 

Kotun mai alkalai uku, wadda ta shafe shekaru biyar tana shari'ar a kan mutane 24 da aka zarga, ta ce nan gaba ne za ta sanar da lokacin yanke hukunci a kan laifin da mutanen suka aikata.

Karin bayani:Amurka ta sake kama jirgin dakon man Iran a tekun Indiya 

Haka zalika kotun ta sallami mutane tara bayan wanke su daga zarge-zargen, yayin da ta ce wani mutum guda kuma ta same shi da aikata karamin laifi.

Edited by:Abdullahi Tanko Bala
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW