Za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi
March 4, 2023Kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci a kan shari'at canjin kudi inda ta umurci babban bankin Najeriya CBN da ya bari a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na Naira dubu 1,000 da 500 da 200 har zuwa ranar 31 ga watan Disamban wannan shekara, abin da ya nuna nasarar da gwamnonin da suka kai kara suka samu a gaban kotun.
Gaba daya dukkanin bukatun da gwamnonin 16 suka gabatar ne a kan wannan sabon tsarin na canjin kudi ta biya masu, abin da ya nuna a fili yadda gwamnonin suka samu gagarumar nasara a kan wannan shari'a ta canjin kudi a Najeriyar.
Murna har baka ga gwamnonin uku da tun farko sune suka fara shigar da karar watau, Nasiru Elrufai na jihar Kaduna da Matawalle na jihar Zamfara da Yahya Bello na ihar Kogi wadanda dukkaninsu sun zo kotun kuma a gabansu aka yanke hukunci.
Duk da narasar da aka samu ana dari-dari a kan matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da babban bankin kasar za su dauka ko za su yi biyayya ga wannan umurmi, domin a baya sun ki bin umurnin da kotun ta bayar, abin da masana shari'a suka bayyana hatsarinsa ga kasa da ke bin tafarki na mulkin dimukurdiyya.