1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta bada belin matashiyar da ake zargi da kone Alqur'ani a Pakistan

September 9, 2012

Kunar littafi mai tsarki a kasar Pakistan kan iya kai ga hukuncin kisa kamar yadda dokar kasar ta tanada.

Life and people of Mehra Jaffer, a village in Islamabad, where Muslim Majority and Christian minority people live together for years until few days ago when few local Muslims accused an 11 year old girl Rimsha of alleged blasphemy. Now, there is tension in the area which also forced many Christian families to leave the village. A girl, who is a neighbor of the arrested girl Rimsha is standing at her doorstep together with her younger brother. Copyright: DW/Shakoor Raheem August, 2012, Mehra Jaffer Village, Islamabad, Pakistan
Rimsha MasihHoto: DW

Sama da makwani 5 kenan da ake ta ci bata ci ba a dangane da maganar Rimsha Masih wata matashiya mabiya addinin krista a kasar Pakistan bayan da hukumomin kasar suka zarge ta da kone alqur'ani. A farkon watan da ya gabata ne wasu mutane suka bada shaidar cewar matashiyar 'yar kimanin shekaru 13 ta kone littafin mai tsarki abunda kuma kan iya kaita ga hukuncin kisa idan har kotun ta tuhume ta da wannan laifin.
To saidai bayanai daga kwararun jami'an likitoci sun yi amanin cewar matashiyar bata taba karatun arabiya ba ko kuma na boko kana tana da tabin hankali. Tuni kuma kasashen duniya suka zuba ido ga hukumomin kasar ta Pakista domin ganin an gudanar da cikaken bincike kamun a hukunta ta.
Kodayake wasu rahotanin daga birnin Islamabad babban birnin kasar sun ce bayan wani bincike ana shakkun wani shehin malamin da kokarin shafa mata kashin kaji domin hura rikicin addini a kasar inda a ke da kwarya kwaryar zaman lafiya tsakanin krista da musulmai.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Abdoullahi Tanko Balla