Kotu ta buƙaci da a yanke wa Mohamed Mursi hukuncin kisa
May 16, 2015Talla
Wata kotu a Masar ta buƙaci da a zartas da hukuncin kisa ga tsohon shugaban ƙasar Mohamed Mursi,tare da wasu ɗaruruwan 'yan Ƙungiyar 'Yan uwa Musulmi waɗanda ake zargi da hannu a fasa wani gidan kurkuku da 'yan kaso suka tsere a lokacin juyin-juya hali na shekara ta 2011.
Kotu ta nemi kuma da a yanke hukuncin na kisa ga jagoran Ƙungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi Khairat El Shater tare da wasu mutane 15 saboda hada baki da wasu jami'an na ƙasashen waje domin tada fitina a cikin ƙasar.