1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu ta bukaci aiki da dokar hana rufa-rufa

Uwais Abubakar Idris SB
April 22, 2025

Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana fafutuka a yanzu kotun kolin Najeriya ta ayyana cewa dokar da samar da bayanai ta aka samar a 2011 a kasar ta zama dole ga daukacin matakan gwamnati da na hukumomi.

Na'urar daukar magana
Na'urar daukar maganaHoto: Rolf Poss/imago images

Wasu kofofi ne suka sake budewa a fanin yaki da cin da rashawa a Najeriya wanda gagarumar nasara ce aka samu bayan kwashe shekaru ana fafutuka na kai wa ga hakan. Wannan ya biyo bayan jajircewa da masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa da ma ‘yan jaridu suka kwashe shekaru 14 suna kai gwauro suna kai mari na ganin sun samu aiki da wannan doka kammar yadda ya dace.

Karin Bayani: 'Yan jarida na aiki cikin wahala a Afirka

Tun bayan kafa wannan doka a 2011 a Najeriyar ne murna ta koma baka musammanb ga ‘yan jaridu da masu fafutukar kare hakin jama'a a Najeriyar, domin an shiga hali na rijiya ta bayar guga ta yi kememe ta hana musamman ga gwamnatocin jihohi da ma wasu ma'aikatun gwamnati da kan fake da cewa sai jihohinsu sun amince da dokar kafin su amince da ba da bayanai. Wannan ya haifara da jihar cikas ga aikin jaridu na bincike da bin bahasin abin da ya faru.

Aikin bincike a kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati musamman kasha kudadden jama'a ya kasance weanda ke da tasiri sosai wajen bakado yadda mutane ke nuna halin bera bisa ga abinda aka basu amana, abinda ya sanya karfafa wannan doka. Usman Babaji na daya daga cikin mutanen da ke wannan aiki a karkashin cibiyar Wikki ya ce akwai batutuwa da dama da wannan mataki zai karfafa.

Bisa halin da ake ciki a Najeriya a yanzu ne aka fi buktar aiki da wannan doka ta samu bayyanai a kasar. Kwararru na bayyana cewa ta hanyar samar da bayanai a kan yadda ake tafiyara da al'ammuran gwamnati zai toshe kafar yaki da cin hanci da rashawa don kaucewa sai an aikata barnar a shiga rufa rufa.