1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu ta ce a bude asusun bankin 'yan #EndSars

Ramatu Garba Baba
February 10, 2021

Wata kotu a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ce, ta bayar da umarni ga babban bankin CBN da ya gaggauta bude asusun ajiyar masu zanga-zangar #EndSars da aka rufe a bara.

Nigeria Lagos | Protest EndSARS
Hoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture-alliance

A wannan Larabar ce kotun da ke Abuja a ta bakin alkali Ahmed Mohammed, ta bayar da umarni ga babban bankin Najeriya da ya gaggauta bude asusun ajiyan masu zanga-zangar #EndSars da aka toshe a bara. Wadanda lamarin ya shafa na daga cikin jagororin zanga-zangar da suka ja ra'ayoyin jama'a a ciki dama wajen kasar.

Umarnin ya biyo bayan cimma matsaya da aka yi, a tsakanin bangaren gwamnati da bangaren wakilan masu zanga-zangar, da zummar rufe babin kazamin rikicin da ya janyo asarar rayuka da salwantar dukiyoyin jama'a da ma na gwamnati kan adawa da jami'an gwamnati da ake zargi da cin zarafin fararen hula.