1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta ce a saki 'ya'yan Hosni Mubarak

January 22, 2015

Kotu a Masar ta bada umarnin sakin 'ya'yan tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak da ake tsare da su saboda laifin cin hanci da rashawa da aka same su da shi a baya.

Al-Sisi bei Hollande 26.11.2014
Shugaban Masar Abdel Fatah al-SisiHoto: Reuters/P. Wojazer

Lauyansu wato Farid el Deeb ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewar a wannan Alhamis din ce kotun da ke zamanta a Alkahira ta bada umarnin sakin Alaa da Gamal daga gidan kason da ake tsare da su saboda babu wata shari'a da yanzu haka ake yi musu.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne kotu a kasar Masar din ta soke hukunci da aka yanke musu na daurin shekaru 4 bayan da aka same da laifi, to sai dai nan gaba Alaa da Gamal din za su sake gurfana gaban kuliya a shari'ar da za a sake musu kan shi wannan batu na cin hanci da rashawa bisa ga wani umarni da kotun daukaka kara ta bada.