Dage zaben gwamna a Adamawa
March 21, 2019Talla
Matakin kotun ya biyo bayan karar da dan takarar gwamna a jam’iyyar MRDD ya shigar kotun, inda yake kalubalantar hukumar ta zabe da rashin sanya alamar jam’iyyar tasa a takardar zaben gwamna da aka yi a ranar tara ga watan nan na Maris kamar yadda wakiliyarmu a Adamawa Fati Muhammad ta sheda wa DW.
Barista Aji Kamale masanin shari'a ne da ya leka kotun da ta zauna a Yola fadar gwamnatin jihar ta Adamawa ya bayyana cewa dakatar da zaben da aka shirya a ranar Asabar ya biyo bayan cewa dan takarar jam'iyyar ta MRDD ya ce ba a sanya alamar jam'iyyarsa ba a takardar zabe. Yayin da ita kuwa hukumar zabe ta ce jam'iyyar ba ta cika sharudan shiga zaben ba.