Kotu ta dakatar da Trump hana baki shiga Harvad
May 23, 2025
Alkalin wata kotun gunduma a Amurka Allison Burroughs, ya yanke hukunci sa'o'i bayan da babbar jami'ar kasar kuma mafi arziki ta shigar da kara idan take kalubalantar matakin gwamnatin kasar na hana ta daukar dalibai daga kasashen waje.
Jami'ar Harvard ta bayar da hujjar matakin da gwamnatin ta dauka na soke shirin musanyar dalibai da cewa "ramuwar gayya ce karara” saboda kin amincewa da bukatun manufofin gwamnatin Shugaba Trump na kyamar baki.
Amurka ta fara tesa keyar bakin haure zuwa gida
Shugaba Donald Trump ya sa zare da jami'ar, bayan da ta ki mika wuya kan matakinsa na sa ido kan baki, inda ya zargi jami'ar da zama mafaka ta kyamar yahudawa.
Jami'ar Harvard ta yaye daliban da suka yi tasiri a duniya, guda 162 daga ciki sun lashe kyautar Nobel.
Trump ya sa lokacin korar baki daga Amurka
Tuni Trump ya yi barazanar dakatar da kudaden tallafin gwamnati ga jami'ar dala biliyan tara, ya kuma sha alwashin tisa keyar wani mai bincike daga makarantar kiwon lafiya na jami'ar daga kasar.