SiyasaJamus
Bajamushe ya taimaka wa kungiyar IS kisan kai
November 27, 2021![Düsseldorf | Urteilsverkündung im Mordprozess gegen den IS-Terroristen Nils D.](https://static.dw.com/image/59951346_800.webp)
Talla
Kotun ta samu Bajamushen da laifin shiga kungiyar ta'addanci ta IS, inda ya yi amfani da wannan damar ya taimaka wurin gallaza wa wasu mutane da IS ta tsare a wani garin kan iyakar Siriya da Turkiyya, lamarin da ya yi ajalin mutane uku a shekara ta 2014.
Masu shigar da kara sun so a yanke wa Bajamushen mai suna Nils D. daurin rai-da-rai amma kotun ta Jamus ta ce ta sassauta masa saboda bai wahalar da shari'a ba a wurin bayar da bayanan ta'addanci.
A shekara ta 2014 dai daruruwan Jamusawa ne suka dauki kayansu suka tafi Siriya, inda suka shiga kungiyar IS wace ta so kafa Daula a Siriya. A baya-bayan nan hukumomin Jamus na kokarin ganin sun hukunta Jamusawan da suka shiga IS da yanzu haka ake rike da su a kasashen Siriya da Iraqi.