Hukuncin daurin rai da rai kan mutane 500
November 26, 2020![Recep Tayyip Erdogan](https://static.dw.com/image/53527232_800.webp)
Talla
Shari'ar ta shafi wasu sojoji da ake zargi da kitsa juyin mulkin a cikin barikin sojoji, tare da ba da umarnin jefa bude wuta a gine-ginen gwamnati. Akalla mutane 251 sun mutu sama da 2,000 sun jikkata a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Mutane 385 sun ba da sheda a shari'a 515 tun bayan fara shari'ar, an yankewa mutane sama da 200 hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, wadanda ake zargin suna da alaka da malamin addinin kasar Fethullah Gülen da ake zargin shi ya shirya juyin mulkin.