Kotu a Rasha ta daure Navalny a gidan yari na shekaru uku
February 2, 2021Talla
Tun daga farko dai alkalai da ke shari'a a kotun sun zargi Navalny ne da taka dokar kotun, bisa yin gaban kansa bayan an masa daurin talala na tsawon shekaru uku a shekarar 2014 a kasar.
Sai dai da yake mayar da martani kan zargin a gabanin hukuncin kotun, Mista Navalny ya musanta zargin karya hukuncin, yana mai bayyana cewa ba zai aminta da daukar laifin ba.
An kama Navalny ne a tsakiyar watan Janeru, bayan ya koma gida sakamakon doguwar jinyar da ya sha a wani asibin da ke nan Jamus saboda shayar da shi wata guba.