SiyasaAsiya
Myanmar: Suu Kyi za ta yi zaman gidan kaso
April 27, 2022Talla
Kotu a Myanmar ta yanke wa hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyidaurin shekaru biyar a gidan kaso bayan samun ta da laifin cin hanci. Hukuncin na wannan Laraba shi ne na farko a cikin zarge-zargen cin hanci da gwamnatin mulkin sojin kasar ke yi wa Suu Kyi.
A shekarar da ta gabata ce dai sojoji suka hambarar da Suu Kyi daga mulki. Idan an hada da hukuncin wannan Laraba da tsohon hukuncin da wata kotun Myanmar ta yanke wa tsohuwar shugabar a baya, a yanzu Suu Kyi za ta yi shekaru 11 ke nan a gidan kaso.