1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Kotun Pakistan ta daure 'yan adawa fiye da 100

Suleiman Babayo AH
July 31, 2025

Kotun Pakistan ta daure masu zanga-zanga fiye da 100 ciki har da jagoran 'yan adawa na kasar shekaru 10 sakamakon zanga-zanga ba bisa ka'ida ba, domin nuna goyon baya ga tsohon Firamnista Imran Khan.

Magoya bayan tsohon Firaminista Imran Khan na kasar Pakistan
Magoya bayan tsohon Firaminista Imran Khan na kasar PakistanHoto: Irfan Ali/Anadolu Agency/picture alliance

Kotu a kasar Pakistan ta daure fiye da mutane 100 da aka samu da laifin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba, a shekara ta 2023 domin nuna goyon baya ga Firaminista Imran Khan da majalisar dokoki ta kada masa kuri'ar yanke kauna.

Karin Bayani: Kotun Pakistan ta daure tsohon firaminista Khan da matarsa

Hannun hagu, jagoran 'yan adawa na Pakistan Omar Ayub KhanHoto: AAMIR QURESHI/AFP via Getty Image

Cikin mutnaen da aka samu da laifi har da jagoran 'yan adawa na kasar Omar Ayub Khan wanda yake jam'iyya daya tare da tsohon Firaminista Khan. An daure mutanen na tsawon shekaru 10.

Shi dai Imran Khan ya kasance firaministan kasar ta Pakistan daga shekara ta 2018 zuwa 2022, kuma majalisar ta kada masa kuri'ar yankar kauna gabanin karewar wa'adin mulkinsa, inda yanzu haka shi ma yake garkame, bisa laifukan da ake gani masu nasaba da siyasa.