Fitar Afrika ta kudu daga ICC ya saba doka
February 22, 2017Talla
Wata kotu a Afirka ta kudu ta yi watsi da shirin gwamnatin na janyewa daga wakilici a kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya ICC ta na mai cewa matakin gwamnatin ya saba doka.
Hukuncin na zama babban koma baya ga shugaban kasar Jacob Zuma kuma labari mai dadi ga kotun ta ICC wadda ke fuskantar baraza ficewa daga wasu kasashen Afirka.
Kasar ta Afirka ta kudu ta baiyana aniyar ficewa daga kotun ta ICC ce sakamakon takaddama kan ziyarar da shugaban Sudan Omar al Bashir ya kai kasar a shekarar 2015 inda ta ki bin umarnin kotun na kama al Bashir, ta na mai cewa yana da kariya a matsayin shugaban kasa.