Ana tuhumar tsohon hafsan Najeriya da cin hanci
March 7, 2016Shi dai Alex Badeh an tsare shi ne a watan Fabarairun da ya gabata bisa badakalar karkatar da sama da naira biliyan uku a shekara ta 2013 da ke zama kudaden da gwamnati ta tanada don tunkarar ayyukan magance matsalolin 'Yan Boko Haram.
Daga cikin tuhumomi 10 da ake masa dai sun hada da cin amana da kuma cire sama da naira biliyan daya daga cikin asusun rundunar sojoji domin amfanin kansa.
Tuni dai hukumar EFCC ta kwace wasu manya-manyan kadarorinsa da suka hada da gidaje a Abuja babban birnin Najeriya.
Tun dai lokacin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya hau gadon mulki a shekarar data gabata yaci alwashin dukkanin wadanda suka yi watanda da kudaden gwamnati musamman ma kudaden da aka kebe don yakar kungiyar Boko Haram an gurfanar da su a kotu.