1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An soke sakamakon zaben Romaniya

Suleiman Babayo ATB
December 6, 2024

Kotun tsarin mulkin kasar Romaniya ta soke sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na farko, saboda kutsen da aka samu daga Rasha da hukumomin tsaron kasar suka tabbatar.

Romaniya | 'Yan takara da suka kai zagaye na biyu a zaben Romaniya, Calin Georgescu da Elena Lasconi
'Yan takara da suka kai zagaye na biyu a zaben Romaniya, Calin Georgescu da Elena Lasconi

Kotun tsarin mulkin kasar Romaniya ta soke zaben shugaban kasa zagaye na farko da aka gudanar a kasar, inda haka yake zuwa kwanaki bayan zargin wani tsararren shiri ta intanet na kasar Rasha domin karfafa yakin neman zaben mai matsanancin ra'ayi da ke goyon bayan kasar ta Rasha. Matakin kotun ya biyo bayan bayanan sirri da Shugaba Klaus Iohannis na Romaniya ya bayar kan katsalandar na Rasha da hukumomin tsaron Romaniya suka bankado.

Karin Bayani: Firamnista Victor Ponta na Romaniya ya yi murabus

Matakin na Rasha ya taimaka wa Calin Georgescu wanda ba sasanne ba, samun nasarar kai wa zuwa zagaye na biyu inda zai fafata Elena Lasconi mai ra'ayin sauyi, sakin yanzu kotu ta soke sakamakon zaben. Hukuncin kotu ya nuna irin yanayin da tsarin duimukaradiyyar kasra Romaniya ya smau kansa.