Shugaba Trump ya bayar da toshiyar baki
January 10, 2025Sai dai duk da cewa alkalin ya kyale zabbane shugaban na Amurka Donald Trump ba tare da yanke masa hukunci ba, hakan ba ya nufin ba a samu shugaban da ake shirin rantsarwa a karo na biyu nan da kwanaki 10 da aikata laifi ba. Da yake mayar da martani kan zaman kotun a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce da man can babu wani laifi da ya aikata. A watan Mayun bara ne kotu ta samu Trump da laifuka 34 na bayar da kimanin dalar Amurka dubu 130 a matsayin toshiyar baki ga wata jaruma a fina-finan batsa, domin samun damar lashe zabensa a shekara ta 2016. Trump dai na zaman mai laifi na farko a tarhin Amurka da za a rantsar a wani babban mukami, har na shugaban kasa da yake shirin dare wa kan madafun iko a ranar 20 ga wannan wata na Janairu da muke ciki.