Kotu ta sauke firaministar kasar Thailand
August 29, 2025
Kotun tsarin mulki ta yanke hukunci cewa Shinawatr mai shekaru 39 ta karya ka'idojin gudanar da harkokin shugabanci a wata tattaunawar waya da aka kwarmata, kuma ta bazu kamar wutar daji a kasar. A bisa wannan dalili kotun a Jumma'ar nan ta ce dole ta sauka daga mukaminta.
Umurnin sauke ta daga mukaminta ya shafi daukacin ministocin kasar, wadanda su ma dole ne su ajiye mukamansu, amma za su ci gaba a matsayin gwamnatin rikon kwarya har sai an kafa sabuwar gwamnati. ‘Yar siyasar ta shaida wa manema labarai cewa ta amince da hukuncin kotun.
Tuni aka ayyana Phumtham Wechayachai, a matsayin firaminista na rikon kwarya da zai kula da harkokin gwamnati har sai majalisa ta zabi sabon shugaban gwamnati.
Wannan hukunci ya zama karo na biyar cikin shekara 17 da kotun tsarin mulkin Thailand ta sauke firaminista daga mukaminsa.