Kotu ta tabbatar da hukuncin kisa a kan Morsi
June 16, 2015A kasar Masar kotu ta tabbatar da hukuncin kisan da ta yanke wa tsohon shugaban kasar mai kishin Islama Mohamed Morsi a watan jiya bayan da ta kama shi da laifin tserewa daga gidan kurkuku a lokacin wani bore da 'yan kaso suka tayar a shekara ta 2011 da kuma tsara kai wasu jerin hare-hare.
Wannan hukunci ya biyo bayan wani hukuncin na daban na kason rai da rai da kotun ta yanke wa tsohon zababben shugaban kasar ta Masar a bisa kamashi da laifin yin leken asirin kasar ta Masar. Da ma a cikin watan Maris din da ya gabata wata kotun ta yanke hukunci zaman kurkuku na tsawon shekaru 20 ga tsohon shugaban Morsi a bisa samunshi da aikata laifin tunzara jami'an tsaro ga yin amfani da karfin tuwo domin murkushe masu zanga-zanga a shekara ta 2012.
Sai dai Mohamed Morsi na da damar daukaka kara a kan illahirin wadannan hukunce-hukunce guda ukku da kotun ta yanke masa.