Kotu ta tabbatar da nasarar Doumbuya
January 5, 2026
Alkaluman farko sun nuna Doumbouyana da kashi 86.72 cikin 100 na kuri’un, inda ta ayyana shi a matsayin shugaban kasar Guinea na wa’adin shekaru bakwai nan gaba.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Guinea ya taya Doumbouya murna tare da cewa Washington na fatan karfafa alaka da inganta daidaiton tattalin arziki.
A wani takaitaccen jawabi da ya yi bayan yanke hukuncin, Doumbouya ya yi kira ga dukkan 'yan kasar a ciki da na kasashen waje, da su hada kai domin gina sabuwar Guinea.
Sakamakon ya nuna Balde shugaban jam'iyyar adawa ta Democratic Front of Guinea ya zo na biyu da kashi 6.59 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Ya bukaci kotun kolin ta soke sakamakon zaben na wucin gadi, yana mai cewa kidayar kuri'un ba ta gaskiya ba ce, kuma an kori wakilan jam'iyyarsa daga wasu rumfunan zabe.
Mutane da dama na sukar zabven bayna kaurace masa sakamakon hana man'yan takara shiga zabe. Doumbouya mai shekaru 42 a duniya, fa fara mulkin kasar tun a 5 ga watan Satumban 2021 bayan juyin mulki, amma yanzu zai sha rantsuwar fara sabon babin shugabanci ba na kaki ba a matsayin shugaban kasar na biyar.