1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu ta tabbatar da Gawuna gwamnan Kano

November 17, 2023

Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun shari’ar zaben gwamnoni tare da mika Kano zuwa ga APC, batu da ke zama gagarumin koma baya ga NNPP mai mulki.

Abba Kabir Yusuf da Dr. Nasiru Yusuf GawunaHoto: Private/Bashir Ahmad/Facebook

Kadan daga cikin yadda ta kaya ke nan a harabar kotun daukaka karar da tai zaman ta anan a Abuja in da kotun daukaka karar zaben jihar ta tabbatar da hukuncin da ya mika jihar zuwa ga Nasir  Yusuf Gawuna.

Kotun a karkashin mai sharia Oluyemi Osadebey ta tabbatar da haramcin kuri'u160,000 da ta ce ba na halas ne ba. Ra'ayi ya zo iri daya a bangaren alkalan cewar daukacin kuri'un basu da shaida ta hukumar zabe, a saboda haka babu hujjar amfani da su wajen hukuncin shari'ar.

Ko bayan manyan jiga-jigan siyasar, kotun dai ta kuma  cika makil da magoya bayan da suka yi tattaki su kuma kuma mamaye daukacin harabar kotun. To sai dai kuma a yayin da masu tsintsiyar suke tsallen murna, a bangare na NNPP mai kayan dadi ranar na zaman ta bakin ciki da bacin rai.

Ko bayan jiharKano da ke a baki na kasa, kotun ta kuma tabbatar da zaben gwamnan Bauchi duk a cikin harabar guda daya. Faruk Mustapha da ke zaman daraktan yakin neman zaben Bala Abdulkadir Mohammed ya ce, nasarar tasu bata da ruwa da tsaki da danyen ganyen da ke tsakanin Bauchin PDP da Abujar da ke zaman ruhin APC.

Ana saran daukaka kara ya zuwa kotun koli a bangaren jihohin guda biyu, kotun kuma da ke zaman matakin karshe cikin gwagwarmaya ta mallaki na ruhi na siyasa ta Jihohin.