Kotu ta tsige Firamiyan Pakistan
June 19, 2012Talla
Kotin ƙolin ƙasar Pakistan ta yanke hukuncin tsige Firaminista Yusuf Raza Gilani daga muƙaminsa.A cikin watan Afirilu Kotun ta zargi Gilani da taka dokokin ƙasa, hasali ƙin bada kai ga tuhumar da kotun ke yi wa shugaban ƙasa Asif Ali Zaradri game da badaƙalar cin hanci ada rashawa.
Saidai masu kula da al'amura a Pakistan na kallon wannan hukunci a matsayin abinda ka iya tada sabuwar fitina cikin ƙasa.Wani mai magana da yawun jama`iyar PPP mai milki mai mulki ya nunar da cewa jam'iyar za cenza Gilani da wani kusa
A yanzu al'umar ƙasa ta zuba ido ta ga abin da zai biyo bayan hukunci, wanda bisa ga alamau zai cilastawa ƙasar shirya saban zaben a farkon shekara mai kamawa.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Umaru Aliyu