1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Kotu ta umurci Isra'ila ta dakatar da yaki a kudancin Gaza

Abdoulaye Mamane Amadou
May 24, 2024

Kasar Isra'ila ta yi fatali da umurnin kotun Majalisar Dinkin Duniya na kan dakatar da yakin da ke yi a kudancin Gaza nan take.

Hoto: Nick Gammon/AFP/Getty Images

Kotun Majalisar Dinkin Duniya ICJ ta bukaci Isra'ila da ta dakatar da kuste da luguden wutar da take yi nan take a yankin Rafah na kudancin Gaza.

A zaman da ta yi na musamman a birnin Hague, kotun ta kuma bukaci kungiyar Hamas da ta gaggauta sakin daukacin 'yan Isra'ila da take garkuwa da su ba tare da wani bata lokaci ba.

Karin bayani : Kotun ICC ta bada sammacin kama Netenyahu da jagororin Hamas

Sai dai a martanin da ta mayar kan wannan kuduri, Gwamnatin Isra'ila ta yi fatali da matakin tana mai cewa samamen da take yi a kudancin Gaza baya shafuwar fafaren hula a sanarwar da ta fitar jim kadan bayan kudrin na kotun Majalisar Dinkin Duniya.

Kasar Isra'ila ta ce tana kiyaye duk wasu abubuwan da ka iya kawo tangarda ga fararen hula a farautar mayakan kungiyar Hamas da take a yankin Gaza.

Karin bayani : Ana tattauna batun sulhunta rikin Gaza a Faransa

Kasar Afirka ta Kudu ce ta shigar da kara tare da neman kotun da ta tilasta wa Isra'ila dakatar da yakin da take yi a yankin, tare da bari a shigar da kayayakin agaji ga Falasdinawan da ke cikin halin taraddadi.