1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta umurci ASUU da ta koma bakin aiki

Binta Aliyu Zurmi
September 21, 2022

Kotun kula da da'ar ma'aikata a Najeriya ta umurci kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU da ta janye yajin aikin da ta ke yi.

Nigeria Bayero Universität in Kano
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/GettyImages

Mai shari'a Polycarp Hamman ya bukaci malaman jami'o'in su koma bakin aiki zuwa nan da dan lokacin da zai yanke hukunci a kan shari'ar da mahukuntan Najeriyar suka shigar da kara a gaban shi.

Sama da watanni 7 ke nan da aka rufe jami'o'i a Najeriya bisa neman karin albashi da kuma wasu alawus-alawus da malaman suka nema daga gwamnatin tarayya.

Wannan matakin na kotu dai na zuwa ne bayan da a jiya dali'bai a wasu sasan kasar suka gudanar da zanga-zangar neman a bude makarantu domin ci gaba da daukar darussa.