1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta wanke tsohon firaministan Nijar Hama Amadou

October 6, 2012

Bayan da aka share kusan shekaru haɗu ana kai ruwa rana a kan batun zargin tsohon firaministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou kotu ta wanke shi.

Hoto: picture-alliance/Photoshot

A Jamhuriyar Nijar kotun ƙolin ƙasar ta wanke Hama Amadou shugaban majalisar dokokin ƙasar ta Nijar a yanzu kana tsohon firaministan ƙasar daga zargin yin sama da faɗi da kuɗaden tallafin ga kafofin yada labarai masu zaman kansu na ƙasar a shekara ta 2001.
Kotun ta wanke Hama Amadou bayan wani dogon zama na kimanin awoyi 14 da ta yi a yimmacin ranar Juma'a a birnin Yamai, wannan kuwa duk da ƙoƙarin da babbar mai gabatar da kara ta gwamnatin ƙasar ta yi na ganin alkalan kotun sun tuhume shi a lokacin wannan zaman na kotu. A kan wannan zargi ne dai mallam Hama Amadou shugaban jam'iyyar Lumana Afirka daya daga cikin manyan jam'iyyun da ke mulki a yau, ya tsinci kansa a gidan kurkuku na garin Kutukale a shekara ta 2008 lokacin mulkin hamaɓararen shugaban ƙasar Tanja Mamadou, inda ya kwashe watanni 10.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mohammad Nasiru Awal