Wata kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa ga Badie
April 11, 2015Talla
Kotun ta yanke masa hukunci ne tare da wasu magoya bayan ƙungiyar su 11 waɗanda aka samu da lafin shirya kai hare-hare da kuma kitsa wa gwamnatin maƙarƙashiya don tayar da fitina.
Kotun dai ta bayyana wannan hukunci ne bayan da ta gabatar da shi ga jagorran addinin ƙasar kamar yadda dokar kasar ta tanada wato Mufti.Sannan kotun ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga wasu mutane su 23 a ciki har'da wani matashin ɗan ƙasar mai asilin Amirka wanda ake tsare da shi tun shekarun 2013.