Suu Kyi za ta yi zaman gidan yari
December 30, 2022Talla
Kotun ta sameta da laifuka guda biyar na cin hanci da karbar rashawa. Hukuncin da aka yanke wa tsohuwar firaministan mai shekaru 77, ya kai jimillar shekaru 33 na zaman gidan yari. Sojoji sun hambarar da zababbiyar gwamnatin Suu Kyi a shekara ta 2021.Masu fafutukar kare hakkin bil' Adama sun hakikance cewa shari'ar da ake yi wa matar da ta taba lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel na da nasaba da siyasa.