Kotu ta yanke wa 'yan Boko Haram 125 hukunci a Najeriya
July 27, 2024Talla
Ofishin atoni-janar na kasar ne ya sanar da haka, yana mai cewa hakan ya biyo bayan wani zama na musamman da kotu ta yi kan mutanen da aka samu da aikata laifin.
Sanarwar ofishin atoni-janar na Najeriyar ba ta zayyana hukunci ko tsawon shekaru na daurin da aka yanke wa masu laifin ba, amma ta ce mutum 85 daga cikinsu an same su da laifin tallafa wa 'yan ta'adda da kudade yayin da mutane 22 aka same su da aikata manyan laifuka da suka saba da tanade-tanaden kotun duniya taICC, sauran kuma an yake musu hukuncin aikata laifin ta'addanci kai tsaye
Kimanin tsofaffin 'yan Boko Haram 400 da a baya aka yanke musu irin wannan hukuncin, an tura su gidan gyaran hali a jihar Gombe bayan da suka kammala zaman kaso na shekarun da kotu ta yanke musu.