Hakkin dan AdamAmurka
Kotu ta yarda Trump ya kori yan Venezuela
May 20, 2025
Talla
Kotun kolin Amurka ta amince wa gwamnatin shugaba Donald Trump kawo karshen kariyar doka ga yan Venezuela kimanin 350,000 wadanda a baya doka ta basu kariya daga yiwuwar korar su daga Amurka.
Alkali daya ne kacal daga cikin alkalan kotun ya nuna rashin amincewarsa.
Alkalan kotun basu baiyana hujjar da suka dogara da ita ba wajen yanke hukuncin kamar yadda aka saba a shari'u irin wannan da aka gabatar cikin gaggawa.
Matakin kotun kolin ya jawo martani daga kungiyoyin farar hula.