Kotu ta yi wa Hama Amadou sakin talala a Nijar
March 29, 2016Talla
Lauyan da ke kare Hama Amadou Boubakar Mossi ya shaida wa manema labarai cewar wannan mataki da kotun ta dauka babu wata tantama cikinsa daga yanzu Hama Amadu yana da izinin zuwa inda ya ga dama. Hama Amadou da ya kasance a matsayin dan takara a zaben shugaban kasar ta Nijar tun a zagaye na farko har kuma ya samu zuwa zagaye na biyu, ya sha neman a yi masa sakin talalan amma abin ya ci turai, inda ma daga bisani wani rishin lafiyar da ya fara cin karfinsa ya yi sanadiyyar fice wa da shi ya zuwa kasar Faransa domin yi masa magani.