1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta yi watsi da zargi fayde da ake yi wa Trump

Abdourahamane Hassane
May 10, 2023

Wata kotu a birnin New York ta samu tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump da laifin cin zarafin wata mata a shekarar ta 1996.

New York | Ex-Präsident Donald Trump vor Gericht
Hoto: Seth Wenig/AP/picture alliance

Alkalan kotun guda tara su dukkaninsu sun amince baki daya cewar Donald Trump ba shi da alhakin aikata fyade kamar yadda tsohuwar yar' jarida E. Jean Carroll ta zargeshi. Kotun ta yanke hukuncin  cewar Trump ya biyata diyyar dala miliyan 5 kan wannan cin zarafi na lalata da aka yi a wani kantin sayar da kayayyaki na New York a shekarar ta 1996 wanda ya bata mata suna. Carroll, mai shekaru 79, ta ta rungumi lauyoyinta tare da zubar da hawaye lokacin da aka bayyana hukuncin