Kotun Arusha ta kammala sauraran Kalan Bagosora
June 1, 2007Kotun mussamman da Majalisar Ɗinkin Dunia ta girka a birnin Arusha na ƙasar Tanzania,domin yanke hukunci, ga mutanen da a ke tuhuma, da alhakin kissan kiyasun da ya wakana a ƙasar Ruwanda, a shekara ta 1994, ta kammala sharia´ar Kalan Theoneste Bagosora, ɗaya daga mutanen da ake ɗauka a matsayin kanwa uwar gami a wannan rikici.
Tun shekara ta 2002 kotun ta fara wannan shari´a, ba tare da yanke hukunci ba.
Kalan Bagosora, da sauran manyan sojoji 3 na ƙasar Rwanda da ake zargi da hannu a cikin wannan ta´asa, sun bayyana wa kotu cewar, ƙage ne ake masu.
Alƙali mai gabatar da shari´a, ya buƙaci ɗaurin rai da rai, ga wannan sojoji 4, to saidaia na sa ran yanke hukuncin ƙarshen a shekara mai zuwa.
Binciken da Majalisar Ɗinkin Dunia ta gudanar, ya gano cewar,Kissan kiyasun da ya wakana a Rwanda, ya hadasa mutuwar mutane dubu ɗari 8, daga ɓangarorin Hutu da na Tutsi.