Kotun Burtaniya ta daure wata alkali kan cin zarafi
May 2, 2025
Talla
Masu gabatar da kara sun ce Lydia Mugambe mai shekaru 50, ta yi amfani da matsayinta na zama mai shari'a a babban kotun Uganda ta hanyar kawo 'yar Uganda zuwa Burtaniya a shekarar 2022 don yin aiki a matsayin kuyanga ba tare da albashi ba.
Karin bayani: Yuganda ta tsaurara matakan kungiyoyi masu zaman kansu
An tuhumi Mugambe da John Leonard Mugerwa, mataimakin babban kwamishina a Uganda na wancan lokaci, a karkashin dokar bautar zamani ta Burtaniya.
Sai dai Mrs Mugambe ta ki amsa laifin da ake tuhumrta ta fadawa alkalan kotun Oxford Crown cewa ba ta taba cin zarafin matar ba.