1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar Isra'ila a kotun duniya

Abdourahamane Hassane SB
February 19, 2024

Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta fara zama shari'ar a game da illar da ta biyo baya a shariance bayan mamayar da Israila ta yi wa yankunan Falasdinawa tun shekara ta 1967.

Kotun Majalisar Dinkin Duniya
Kotun Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

 

Wannan sharia'a wacce ita ce irin ta, ta farko da kotun duniyar ke yi, ta kira kasashen kusan 52 domin su zo su ba da shaida. Kasashen Amurka da Rasha da China da sauransu za su yi jawabi ga alkalan yayin zaman kotun da za a kwashe tsawon mako guda ana yi a birnin The Heague na kasar Netherlands. A ranar 31 ga Disamba, na shekara ta 2022, Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani kudurin da ya bukaci kotun ta ICJ da ta gudanar da shari'a a kan batun. Kudirin ya samu amincewar kuri'u 87 da aka kada a zauren Majalisar yayin 26 suka hau kujerar naki kana wasu da 53 suka kaurace, inda kasashen yammacin duniya suka rarrabu a kan batun yayin da kasashen Larabawa suka kada kuri'ar amincewa.

Karin Bayani: Kotun MDD ta umurnci Isra'ila ta kare fararen hula a Gaza

Kotun duniyaHoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

Wadannan kararrakin sun sha bamban da na baya-bayan nan da Afirka ta Kudu ta gabatar tana mai cewa hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza sun sabawa yarjejeniyar kariya. Wannan kara na majalisar ta bukaci kotun ta ICJ ta yi la'akari da abin da mamayar Isra'ila ta haifar a Falasdinu na ci gaba da take hakkokin al'ummar Falasdinu a tsawon mamayar yankin  tun daga 1967. Sannan kotun za ta yi nazarin da nufin gyara ga matsayin birni mai tsarki na Kudus.

A watan Yunin shekarar ta 1967 Isra'ila ta kaddamar da yakin kwanaki shida, inda ta kwace yammacin kogin Jordan da gabashin birnin Kudus daga kasar Jodan, da tuddan Golan daga Siriya, da zirin Gaza da kuma zirin Sinai, lamarin da ya yi illa ga Masar. Daga nan ne Isra'ila ta fara mamaye yankin da ya kai murabba'in kilomita dubu 70,000 na yankin Larabawa, mamayen da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin haramtacce.

Ana kuma bukatar kotun ta ICJ da ta yi nazari kan sakamakon abin da kudurin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a matsayin karan tsaye da Isra'ila ta yi na nuna kin amincewa da dokokin majalisar. Dole ne ta ba da ra'ayi game da yadda ayyukan Isra'ila suka shafi matsayin doka na mamaya da sakamakon ga Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe.

Jinkai a ynakin Zirin Gaza na FalasdinuHoto: Karam Hassan/Anadolu/picture alliance

Kotun za ta yanke hukunci  kan wannan shari'ar, mai yiwuwa a ƙarshen shekara. A baya dai kotun ta ICJ ta bayyana hukunci na bayyana matsayinta kan halaccin ayyana 'yancin kai ga Kosovo a shekara ta 2008 daga Sabiya, da kuma yadda Afirka ta Kudu ta mamaye Namibiya a karkashin mulkin wariyar launin fata. Haka kuma a shekara ta 2004 ta fitar da wani hukuncin inda ta ce wasu sassan katangar da Isra'ila ta gina a yankunan Falasdinawa da ta mamaye ya sabawa doka kuma ya kamata a rushe su. A halin da ake ciki Isra'ila ta ce ba za ta halarcin zaman shariar ba, ta kuma mayar da martani cikin fushi kan kudurin Majalisar Dinkin Duniya, inda Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya kira abin kyama. Amurka da Birtaniya da kuma Jamus sun nuna adawa da kudurin sannan Faransa ta kaurace.