Kotun duniya ta yanke hukunci karo na biyu
December 18, 2012Talla
Kotun duniya mai hukunta masu laifukan yaƙi da ke Hague na ƙasar Holland, ta wanke tsohon madugun 'yan tawayen Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kongo, Mathieu Ngudjolo Chui daga laifukan yaƙi da aka tuhume shi.
Hukuncin na wannan Talata ya kawo ƙarshen tuhumar da ake yiwa tsohon jagoran 'yan tawaye ɗan shekaru 42 da haihuwa. Kuma tun da fari an zarge shi da aiwatar da kisan ƙare dangi ga daruruwan mutane, cikin yankin gabashin ƙasar ta Kongo, da fyaɗe wa mata waɗanda aka aiwatar cikin shekara ta 2003.
Wannan shi ne karo na biyu da kotun ta duniya ta yanke hukuncin tun kafa ta shekaru Goma da su ka gabata.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi