1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ECOWAS ta yi watsi da karar Nijar

Abdul-raheem Hassan Abdoulaye Mamane
December 7, 2023

Gwamnatin mulkin soji ba ta da hurumin kalubalantar duk wani mataki da kungiyar ECOWAS ta dauka don kare tsarin dimukuradiyya tsakanin mambobin kasashenta a yammacin nahiyar Afirka.

Shugaban ECOWAS, Bola Ahmad TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a Nijar a watan Yuli na shekarar 2023, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ta dauki matakin rufe iyakokinta da Nijar, a wani mataki na nuna fushi kan yi wa dimukuradiyya karan tsaye.

Matakin ya haifar da matsin tattalin arziki da taikaita sauran harkokin gudanarwa a cikin Nijar, wannan ya sa gwamnatin sojin ta gurfanar da kungiyar ECOWAS a gaban kotunn kungiyar da ke Abuja da zimmar samun damar dage mata takunkumin karya tattalin arziki.

Karin Bayani: ECOWAS za ta taimaki kasashe

Kafin a kai ga wannan mataki, kungiyar ECOWAS ta sha kai ruwa rana don ganin an shawo kan matsalar siyasa da ta rincabe a Nijar amma sun gaza samun bakin zaren warware rikicin, a matakin farko, sojojin sun ki ba da kofa na tayin tattaunawa da wakilan kungiyar ECOWAS, da ma yunkurin kungiyar na sake dawo da Mohamed Bazoum kan madafan iko.

ECOWAS ta sha yin barazanar daukar matakan soji kan gwamnatin Nijar din muddin ta ki mika wuya na wa'adin mayar da kasar kan tafardin dimukuradiyya, na baya-bayan nan dai shi ne matsin lamba da kungiyar da sauran kasashen duniya ke yi wa sojin Nijar na ganin an sako tsohon Shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Karin Bayani: Sojojin Nijar sun zargi Bazoum da yunkurin gudu

Yanzu haka dai wasu 'yan kasar Nijar sun fara daukar wasu dabaru na samun mafita kan matsin rayuwa na karancin abinci da kudade da magunguna da ake ciki sakamakon rufe iyakokin kasar da wasu kasashe membobin kungiyar UEMOA masu amfani da kudin bai daya na CFA.

Kasar ta zama memba a rukunin kasashe uku na Mali da Burkina Faso da Nijar da suka bullo da sabon kawancen tsaro na AES don mayar da martani gaECOWAS da UEMOA da suka kakaba musu takunkuman karayar tattalin arziki.

Juyin mulki na Nijar ya biyo bayan ikirarin sojin kasar na cewa kasar na fuskantar rashin tsaro na kungiyoyin ta'adda, kuma wannan ba shi ne karon farko da kasar ke fuskanci juyin mulki daga sojoji ba. 

Karin Bayani: Nijar ta soke kawancen tsaro da tarayyar Turai 

Haryanzu babu alamu na lokaci da sojojin suka shirya gudanar da zabe a Nijar don sake mika mulki zuwa farar hula, amma tun bayan juyin mulkin kasar tana fuskantar jerin zan-zangar masu adawa da masu goyon bayan halin da kasar ke ciki.