1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ECOWAS za ta yanke hukunci kan makomar takarar Sonko

November 6, 2023

Kotun ECOWAS ta sanar da cewa za ta yanke hukunci a ranar 17 ga watan Nowamba a game da kila wa kala kan takarar dan adawan Senegal Ousman Sonko a zaben shugaban kasar na 2024.

Senegal Oppositionsführer Ousmane Sonko
Hoto: Seyllou/AFP

Lauyoyin da ke kare dan adawan da ya shiga takun saka da gwamnatin Macky Sall ne suka shigar da kara a gaban kotun mai ofishi a birnin Abuja na Najeriya domin neman a wankesa daga tuhume-tuhume da ake yi masa, wadanda ka iya hana masa tsayawa takara.

Karin bayani:An tsare madugun adawar Senegal Ousmane Sonko a gidan yari 

Dama dai a ranar 12 ga watan Oktoba da ya gabata wani alkali a birnin Ziguinchor da ke Kudancin Senegal ya soke matakin hanawa Ousman Sonko tsayawa takara a zaban shugaban kasar da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabaru na shekarar 2024 mai kamawa.

Karin bayani: Jagoran adawar Senegal na sake yajin cin abinci

Wannan dambarwa dai na zuwa ne yayin da ya rage makwanni uku kacal a rufe karbar takardun takarar shugabancin kasa, to sai dai lauyoyin da ke kare Sonko mai shekaru 49 da haihuwa sun ce ya zama wajibi a gaggauta zartar da hukuncin da alkalin Ziguichor ya yanke don kadda loakaci ya kure.