1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Za a ci tarar kasar Poland bisa rashin dakatar da shirinta

Abdoulaye Mamane Amadou
October 27, 2021

Kotun nahiyar Turai ta yanke hukuncin ladabtarwa ga kasar Poland na cin tara bisa rashin dakatar da tsarinta da ta kira na inganta kotun kolin kasar mai cike da cece-kuce.

Luxemburg | Europäischer Gerichtshof: EuGH-Urteil zum ungarischen NGO-Gesetz
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Immanuel Bänsch

Kasar Poland ta jima ta na 'yar tsama da EU tun bayan da shugaban gwamnati Mateusz Morawiecki ya kudri anniyar kawo muhimman sauye-sauye a fannin kotun kolin kasar, lamarin da kuma kungiyar EU ta kira da rashin adalci da ma tauye cikakken 'yancin alkalai.

Ko farkon wannan watan ma sai da kotun tsarin mulkin Poland ta yi fatali da wasu kudirorin da suka shafi kungiyar ta tarayyar Turai, tana mai cewa sun yi hannun riga da kundin tsarin mulki.

Sai dai matakin kotun da kotun ta dauka a wannan Laraba, ya zo ne daidai da bukatar hakan da tun daga farko hukumar zartarwar EU din ta shigar, tana mai fatan ganin an dauki tsauraran matakai da ta kira na kare mutucin alkalan kotu.