1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Faransa: Samun Sarkozy da laifin cin-hanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 18, 2024

Kotun daukaka kara ta karshe a Faransa ta tabbatar da laifin cin-hanci da rashawa a kan tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy tare da umartarsa da ya sanya sarkar da za ta rinka nuna inda yake har tsawon shekara guda.

Faransa | Kotu | Hukunci | Tsohon Shugaban Kasa | Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas SarkozyHoto: Bertrand Guay/AFP/Getty Images

Tsohon shugaban Faransan Nicolas Sarkozy ne dai shugaban kasa na farko da ya taba fuskantar irin wannan hukunci, bayan da tun da farko aka same shi da laifin bin haramtacciyar hanya da nufin neman taimako daga alkali. Tuni dai lauyansa Patrice Spinosi ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Fransa na AFP cewa Sarkozy zai mutunta hukuncin kotun, koda yake ya ce za su iya daukaka kara cikin 'yan makonni zuwa Kotun Kare Hakkin dan Adam ta Tarayyar Turai EU. A shekara ta 2021 ne dai wata karamar kotu ta same Sarkozy da tsohon lauyansa Thierry Herzog da laifin kokarin hada baki tare da bayar da cin-hanci ga Alkali Gilbert Azibert domin samun bayanai kan tuhumar da ake masa, sai dai har kawo yanzu mai shekaru 69 a duniya Sarkozy bai amsa laifin ba kuma lauyansa ya ce zai ci gaba da fafutuka.