Kotun ICC na hakon shugaban kasa Sudan
December 12, 2010Talla
Shugaban babbar Kotu kasa da kasa dake hukumta mayan laifufuka na yaki Luis Moreno Ocampo .Yayi gargadin cewa nan ba da dadewa ba Kotu ta ICC zata dakatar da shugaban kasar Sudan Omar Hassan El Bashir.Mista ocampo dake magana a wani zaman taron na Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a karshen mako ya ce suna hakon shugaban na sudan. Na gaba ne a ranar Larba mai zuwa Elbeshir zai hallarci wani taro a kasar Zambiya sanan a cikin watan Feberu ya je kasar Senegal.Tun a shekara ta 2009 kotun ta gabatar da wata takarda so muchi ta dakatar da El Beshir akan zargin aikata kisan gila ,dakuma take hakin bil adama a yankin Darfur dake a yammancin kasar Sudan dake fama da yakin basasa.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu