1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfghanistan

Kotun ICC ta bada sammacin cafke jagoran gwamnatin Taliban

July 9, 2025

Kotun Hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ICC, ta ba da sammacin kama jagoran gwamnatin Taliban Haibatullah Akhundzada da alkalin alkalai Abdul Hakim Haqqani, sakamakon zargin keta hakkin mata a Afghanistan.

Dalibai mata a Afghanistan kafin a haramta musu karatu
Dalibai mata a Afghanistan kafin a haramta musu karatuHoto: Ebrahim Noroozi/AP/picture alliance

Kotun ta ICC na zargin jagoran Taliban da alkalin alkalai Abdul Hakim Haqqani, bisa aikata laifin keta hakkin bil Adama ciki har da hana mata 'yanci da duk wata walwala na gudanar da harkokinsu da kuma hana su damar zuwa makaranta da aiki tare da nuna musu wariya dangane da jinsinsu.

Karin bayani: Taliban ta haramtawa gidajen talabijin amfani da bidiyo

Kotun da ke birnin The Haque na zargin Taliban da aikata ta'asar tun daga lokacin da suka hau kan mulki a ranar 15 ga watan Agustan 2021 har zuwa 20 ga watan Janairun 2025. To sai dai mai magana da yawun gwamnatin Taliban  Zabihullah Mujahid ya yi watsi da wannan zargi na ICC, inda ya ce kasar ta Afghanistan za ta ci gaba da bin dokokin addinin Islama sau-da-kafa.

Karin bayani: Kabul: Gangamin adawa da haramta wa mata jami'a

A shekarun baya bayan nan kotun ICC ta bada sammacin cafke shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.