ICC ta ce ana ci gaba da tafka laifukan yaki a yankin Darfur
July 11, 2025
Mataimakin mai shigar da kara na kotun, Nazhat Shameem Khan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya tare da bayyana cewa irin wahalhalun da fararen hula ke fuskanta a yankin Darfurya kai matakin da ba za a amince da shi ba saboda rashin ruwa da abinci.
Shameem Khan ya ce yunwa ta karu inda ake kai wa ayarin motocin jin kai da kayayyakin more rayuwa hari.
Mataimakin mai shigar da kara na kotun ICC ya bayar da misali da karuwar kungiyoyin masu dauke da makamai a Sudan da kuma karuwar ayyukan fyade da cin zarafin mata da kuma yin garkuwa da su.
Yakin Sudan da aka fara shi a watan Afrilun 2023 ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 40,000 yayin da wasu miliyan 13 suke gudun hijira a kasashe makwabta.
Karin Bayani:RSF ta halaka fararen hula da dama a Sudan