1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC ta ce ba a yi kisan kiyashi a yakin Balkans ba

Muntaqa AhiwaFebruary 3, 2015

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta ce ba a aikata kisan kiyashi a yakin da aka yi a yankin Balkans ba.

Internationaler Gerichtshof (IGH) in Den Haag
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Maat

Kotun hukunta muyagun laifuka ta duniya dake a birnin Hague, ta fada yau Talata cewa ba a aikata kisan kiyashi ba, a yakin da aka gwabza tsakanin Sabiyawa dama Kuroshiyawa a rusasshiyar yankin Yugoslavia cikin shekarun 1990.

Shugaban Kotun Peter Tomka y ace dukkanin bangarorin biyu sun aikata laifuka lokacin yakin sai dai babu wani daga cikin su da zai dauki laifin kisan kiyashi. Ministan shari'a a kasar Sabiya Nikola Selkovic ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa, wannan hukuncin ya bude sabon babi ga al'umomin biyu. Dama dai angarorin biyu, sun yi fatar hukuncin zai kaiga kyautata dangantaka a tsakaninsu, kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya sanar.