1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Shekaru 20 da kafa kotun ICC

October 19, 2023

A yayin da Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ke cika shekaru 20 da kafuwa, a ana sa ran za ta fara sauraron koken daya daga cikin mutanen da ake zargi da laifukan cin zarafin dan Adam a Darfur.

Sudan | ICC | Darfur | Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman
Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman zai gurfana gaban ICCHoto: International Criminal Court/AA/picture alliance

Shari'ar ta yanzu dai, na da nasaba da sabon rikicin madafun iko da Sudan din ke ciki a yanzu.  Wajibi ne dai Ali Muhammed Ali Abd-Al-Rahman ya gurfana a gaban Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa wato ICC da ke birnin The Hague, bisa zarginsa da aikata laifuffukan yaki har 31 da suka hadar da hare-haren da ake kai wa fararen hula da fyade da kisan gilla. A cewar tuhumar da ake yi masa, ya aikata wadannan laifuka ne a matsayinsa na babban jagoran mayakan Janjaweed a Darfur daga watan Agustan 2003 zuwa Afrilun 2004. Janjaweed dai mayakan sa-kai ne da suka rika afkawa kabilun Afirka da kungiyoyin 'yan tawaye a bangaren gwamnati, a lokacin yakin da aka yi a Darfur. Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya daga shekara ta 2008, sun nuna cewa wannan rikici ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 300. Daga bisani, wannan yakin ya haifar da abin da ake kira Rapid Support Forces (RSF).
Rashin hukunta masu aikata laifuka a lokutan yakin na bayar da kafar ci gaba da cin zarafin al'umma, a cewar Elise Keppler ta kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch. Sai dai babban mai shigar da karar bai damu da halin da Sudan ta kasance shekaru 20 da suka gabata ba kawai, har ma halin da ake ciki a yau. A wani jawabi da ya gabatar a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a watan Yuli Karim Khan ya bayyana cewa yana ci gaba da gurfanar da masu aikata laifukan yaki a kasar, inda ya jaddada cewa duk wanda ya aikata laifukan cin zarafin dan Adam ko kuma kisan kiyashi za a yi bincike a kansa. A watan Afrilun ne dai fada ya barke tsakanin sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) karkashin jagorancin Janar Mohammed Hamdan Dagalo da aka fi sani da Hemeti, rikicin da ya jefa kasar cikinhalin tasku.

Babban mai shigar da kara a kotun ICC Karim KhanHoto: EBRAHIM HAMID/AFP
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani