Jagorar kasar Myanmmar tayi tsokaci kan kabilar Rohingya
September 19, 2018Tun da fari dai gwamnatin kasar Myanmar ta bayyana cewar rikicin ya samo asali ne a ranar 25 ga watan Agustan shekara ta 2017, yayin da daruruwan mayakan Rohingya suka kaddamar da wani hari kan ofisoshin yan sanda 30 da ke jihar Rakhine, lamarin da ya yi sandiyyar rasa rayukan jami'an tsaro 13, kafin daga bisani sojojin kasar su mayar da martanin hari wanda kuma suka yi wa lakabi da korar 'yan ta'adda daga kasar Myanmar. Shaidun gani da ido dai sun bayyana irin yankan ragon da Sojojin suka yi wa farar hula bayan bankawa kauyukan kabilun na Rohingya wuta.
A nata bangaren jagorar siyasar kasar ta Myanmar Aung San Suu Kyi, a karon farko da ta yi magana kan wannan yamutsi, ta bayyana cewar a shirye take ta karbi wasu daga cikin al'ummar Rohingyan da suka bar kasar da zarar an tantance su. Ana cigaba da Allah wadai da shugabar, sakamakon cigaba da nuna halin ko in kular da take yi da batun cin zarfin kabilar ta Rohingya.