1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC ta Tuhumi Thomas Lubanga

March 14, 2012

Tsohon jagoran ƙungiyar yan tawayen na iya fukatar hukumcin ɗaurin rai da rai a gidan kurku

Congolese warlard Thomas Lubanga (C) is seen behind his lawyers in the courtroom of the International Criminal Court (ICC) at The Hague March 14, 2012. The ICC on Wednesday found Lubanga guilty of war crimes in its landmark first ruling since it was set up a decade ago. Lubanga was accused of recruiting and deploying child soldiers during a five-year conflict until 2003. REUTERS/Evert-Jan Daniels/Pool (NETHERLANDS - Tags: CRIME LAW POLITICS)
Hoto: Reuters

Babbar kotun duniya da ke hukumta mayan laifukan yaƙi ta sami tsohon jagoran ƙungiyar yan' tawaye ta FPLC force Patriotique Pour la Liberation de Congo Thomas Lubanga,da laifin yin amfani da ƙannanan yara a matsayin soji a yaƙin da aka yi na ƙabilanci a lordin Etui da ke a yankin arewa maso gabashin jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a shekarun 2002 da 2003.

Da ya ke yi magana a lokacin da ake gudanar da sharar da ya jagorantar a birnin Hague ,alƙalin mai gabatar da ƙara Adrian Fulfpord ya ce nan gaba za a baiyana hukumci dangane da laifin da ake tuhumar mista lubunga sannan kuma yaƙara da cewar ''ya ce zauran shara'a baki daya ya yanke wannan shawara ta tuhumar mista Lubanga akan waɗanan laifuka. Lubunga ɗan shekaru 51 da haifuwa wanda ke sanye da fara gariya da hula fara ya riƙa murmushi a lokacin da alƙalin kotun ta ke karanto laifufukan da aka tuhume shi da aikata.ƙungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights Wacth ta ce wannan wani sako ne mai ƙarfi ga sauran masu manyan laifukan yaƙi wannan dai shine karo na farko da kotun ta ICC ta yanke hukumci tun da aka kafa ta a shekara ta 2003.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar